Rundunar Sojin Najeriya Ta Kama Wanda Ya Kashe Janar Shuwa A Kano

0
1163

Imrana Abdullahi Daga Kaduna

RUNDUNAR sojojin Najeriya ta bayyana kame wanda ya kashe fitaccen soja da ya shugabanci runduna ta daya a lokacin yakin basasa wato Janar Mamman Shuwa.

Janar Mamman Shuwa,ban da kasancewarsa wanda ya jagoranci rundunar soja ta daya kuma  ya jagoranci runduna ta daya a lokacin da aka yi yakin basasa.

Amma duk da wannan kokari da ya sa Shuwa ya zama gwarzo a duniya sai da aka samu wani ya bindige shi a gidansa da ke Maiduguri ta Jahar Barno a ranar 2 ga watan Nuwambar shekarar 2012.

A sakamakon hakan ne sojojin Najeriya suka shiga bincike har Allah ya ba su nasarar kame wanda ya yi kisan gillar a kan babban sojan.

Kuma mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya Kanar Sani Usman Kuka Shaka, ya bayyana cewa za su sanar da manema labarai a can Kano din yadda aka yi da inda aka kama shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here