Rabo Haladu Daga Kaduna
GWAMNONIN arewa sun nuna damuwa a bisa kashe-kashen
da ya faru a Agatu ta Jahar Binuwai da kuma ta Jahar Enugu.
Gwamnonin na arewa wadanda suka ce sun tattauna wannan batu a taron da suka yi a
Kaduna, sun kuma nuna takaicin su dangane da yadda wasu ke dora alhakin kashe-kashen a kan Fulani makiyaya .
A ganin gwamnonin dora tsana da kiyayya a kan wata kabila ba wata hujja kwakkwara ,ba
zai tabbatar da hadin kai da zamantakewa tagari da ake bukata a kasar nan ba.
Gwamnan Jahar Borno Alhaji Kashim Shettima, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin
na arewa ya shaida wa manema labarai cewa a matsayin fulani \’yan kasa dole
ne su kare mutuncin su, ya ce ba abu ne mai kyau ba a ce koyaushe abu ya faru sai a ce fulani ne.