Daga USMAN NASIDI
WANI mutum mai suna Mamman Dankarami, da ke garin Goru a cikin karamar hukumar Arewa da ke Jihar Kebbi ya yi wa ‘ya’yansa yankan rago da hannunsa.
Rahotanni na nuna cewa wannan yaran nasa dukkanin su maza ne daga dan wata biyar da haihuwa zuwa ‘yan shekara uku da haihuwa.
Da yake bayyana wa manema labarai, shugaban riko na karamar hukumar Arewa, Alhaji Muhammadu Dan Kaku a garin Birnin Kebbi ya ce, bayan mutumin ya kammala kashe yaran nasa sai ya fada cikin rijiya da zimmmar shi ma ya kashe kansa sakamakon ta’asar da ya ga ya aikata, amma da yake Allah ,ya sa wasu jami’an ‘yan sanda da sauran jama’a, na kusa sai aka ceto rayuwar mutumin bayan ya fada rijiyar.
Shugaban ya ce yanzu haka an garzaya da mutumin asibitin kula da masu tabin hankali da ke garin Jega domin duba lafiyarsa, saboda jama’ar da ke unguwar sun tabbatar wa da hukuma cewa mutumin ba shi da cikakken hankali.
Da aka tuntubi hukumar ‘yan sanda ta Jihar Kebbi ko suna da labarin aukuwar wannan lamari, mai magana da yawun hukumar, Nafiu Abubakar ya tabbar da aukuwar lamarin.
Top of Form
Bottom of Form