Rabo Haladu Daga Kaduna
Shugabannin Fulani a Najeriya sun ce wasu mutane ke yin sojan-gona suna aikata laifuka sannan su dora alhakin
hakan kan \’yan Fulani.
Shugabannin sun yi wannan bayani ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zargin Falani makiyaya, game da hannu a aikata miyagun laifuffuka kamar kai hare-hare, da fashi da
makami, da fyade.
Sarkin Fulani na shiyyoyin kudu maso gabas da kudu maso kudancin Najeriya, Ardo Sa\’idu Baso, ya shaida wa manema labarai cewa ko da ya ke a wasu lokutan Fulani na aikata laifuka, amma
yawancin lokuta ba su ne ke aikatawa ba.
A cewarsa, \”Ba ma jin dadin yadda ake danganta duk wani ta\’addanci da \’yan Fulani.Akasari mu ake cutarwa.Wani lokaci idan mun yi bincike muna gano cewa ba \’yan Fulani ne ke aikata miyagun laifuka ba\”.
Ardo Sa\’idu Baso ya amince cewa akwai bata- gari a cikin Fulani, yana mai yin kira a gare su da su daina aikata laifuka.