Hana Bumburutu: Jama\’a Sun Fara Dandana Kudarsu A Kano

0
1678

Jabiru A Hassan, Daga Kano.

MASU ababen hawa a Jihar Kano sun koka kan dokar hana sayar da mai a jarkoki  saboda matsalar da hanawar za ta haifar a kokarin da ake yi na kawar da karancin man fetur a kasar nan.

Wakilinmu wanda ya gudanar da wata tattaunawa da masu ababen hawa a Kano, ya ce mafiya yawan wadanda suka zanta da shi sun nuna rashin jin dadinsu bisa yadda rundunar \’yan sandan kasar nan ta ba da sanarwar hana sayar da mai a jarkoki, lamarin da ka iya jefa kasa cikin wani mawuyacin hali fiye da yadda abin yake a yanzu.

Iliya direban Bas, ya ce ya kamata a fara samar da mai a kowane gidan mai na kasar nan kafin a hana sayar da shi a jarkoki musamman ganin cewa wadatarsa a gidajen mai zai sanya a sami saukin karancin da yake yi a halin da ake ciki, sannan  ya yi fatar cewa nan gaba kadan al\’amura za su inganta a kasar nan.

Tuni dai uwar kungiyar dillalan man fetur reshen Jihar Kano ta umarci \’ya\’yan ta da su daina sayo mai mai tsada domin kada su  hadu da fushin hukuma na kwace masu man da suka sayo da tsada domin sayarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here