


KAMAR dai yadda masu karin magana kan ce \’\’ta faru ta kare wato wai an yi wa mai zani daya sata\’\’,kwarai za a iya cewa a yau dai lamarin da aka dade ana ta ka-ce-na-ce a kansa a game da batun kasafin kudin 2016 ya zo karshe inda shugaban kasar tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya wa kasafin kudin bana hannu kamar yadda za ku iya gani a cikin hotuna a yau Juma\’atu babbar rana, Allah Ya datar da mu baki daya, amin.