Jabiru A Hassan, Daga kano.
RUNDUNAR \’yan sanda ta Jihar Kano ta sanar da cewa ba a yi asarar rai ba a rikicin da ya faru ranar zaben cike gurbi na karamar hukumar Minjibir.
A cikin sanarwar, wadda kakakin rundunar, Malam Magaji Musa Majiya ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai, ya nunar da cewa babu kisan kai a rikicin sannan wadanda ma suka sami raunuka tuni aka sallame su daga asibitocin da suke bayan sun murmure.
Bisa haka ne rundunar ta bukaci kafafen yada labarai da su rika tantance rahotanni da labarai kafin su fitar da su domin tabbatar da sahihancin su a kodayaushe.