Imrana Abdullahi Daga Kaduna
RUNDUNAR\’yan sandan tarayyar Najeriya ta samu nasarar kame wadansu masu satar mutane da suka yi gungu a wasu wurare a Jihar Kaduna.
Sun dai samu nasarar tarwatsa masu satar ne inda wasu suka tsere amma rundunar ta lashi takobin samo wadanda suka tseren.
Rundunar \’yan sandan sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai.
Wadanda aka kaman sun hada da jagoran su Kashemu Shehu da ake kira da Balingo sai Aliyu Mati da ake cewa Yellow da Muhammadu Mamman da Hassan Bello da Bala Muhammed da kuma Ishiaku Kabiru, an kuma same su ne a kauyen Dutse garin Kaduna da Zariya.
Rundunar ta kuma sha alwashin ganin ta tsarkake kasar daga ayyukan irin wadannan mutane.