Imrana Abdullahi Daga Kaduna
AN bayyana kokarin yakar cin hanci da karbar rashawa da cewa samun yin maganinsu shi ne gyaran halayyar jama\’a.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani tsohon dan jarida kuma malamin jami\’a Alhaji Muhammad Haruna, inda ya ce duk wadansu matakan da ya dace gwamnati ta dauka tuni an dade da aiwatar da su amma lamarin sai baba ta gani don haka kowa ya yi kokarin gyara halayyarsa a duk inda ya samu kansa ko a wurin aiki ko kuma a yanayin wata mu\’amala shi ne kadai hanyar gyara.
Ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala tattaki da \’ya\’yan kungiyar NUJ reshen Jihar Kaduna tare da wata kungiya da kuma matasa suka yi daga titin shatale-tale na ofishin shiyya na hukumar samar da hasken wutar lantarki kasa zuwa shatale-tale na Libentis da ke babbar kasuwar cikin garin Kaduna, suka dawo cibiyar \’yan jaridu ta Kaduna inda daga nan aka gudanar da kasidu da dama.
Haruna ya ci gaba da cewa lallai sai kowa ya rika yi wa kansa hisabi ta hanyar ajiye kai a cikin ma\’auni game da batun cin hanci da karbar rashawa.
Wakilin ministan yada labarai na tarayyar Najeriya Alhaji Lai Muhammad, Wanda Malam Hamza Audu mataimakin Darakta a hukumar wayar da kawunan jama\’a ta kasa NOA ya wakilta cewa ya yi babban abin da make nufi da canji ba wai mutane su shiga wahala ba ne sai dai kokarin kawo gyara shi ne manufa.
Da yake tofa albarkacin bakinsa Lauya Pestus Okoye ya bayyana wasu masu sana\’ar cin hanci da karbar rashawa da cewa sun rigaya sun zama masu laifi na kasa da kasa da suka kware ta aiwatar da lamarin a zamanance.
Don haka ya yi kira ga gwamnati da ta tabbatar ta dauki kwararrun mutane a matsayin ma\’aikatan da za su yi yaki ta fuskar cin hanci da rashawa.
Ya bayar da misali da kansa inda ya ce a matsayinsa na Lauyan da ya kwashe shekaru 30 yana aiki, ta yaya za a dauki wanda ya kammala makaranta da satifiket wai ya zo ya yi masa tambayoyi? To mene ne zai tambaye ni?
Daga nan sai Lauya Okoye ya kawo shawarar cewa gwamnati ta samu dokar da za a yi amfani da ita domin yin hukunci ga Lauyoyin da suke taimaka wa masu kwashe dukiyar gwamnati su mayar da ita ta su haka kawai.
\”To ina ga wadanda suka aikata laifin sace dukiyar kasa da a kodayaushe suna da wata hanyar da za su kauce wa laifin da ake tuhumarsu da shi.
Don haka wani al\’amarin kuma shi he samun horo na musamman a kai a kai kuma duk hukumomin da suke aikin yakar \’yan rashawa sai sun kammala duk abin da ya dace kafin su kamo wanda ake zargi saboda tsarin mulki da ya ce a kai wanda ake tuhuma kotu da an kama shi musamman idan akwai kotu a tsawon wuri mai kilomita 40 in kuma babu a kai shi a cikin awoyi 24 wato kwana daya.
Wani da ya wakilci shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu a wajen taron ya ce an taba zuwa gidan wani da ake tuhuma ana bincike aka samu kudi Dala miliyan daya a ajiye amma da mutumin da Lauyoyinsa suka ce ba nasa ba ne. Kuma an samu mutum a Najeriya da ya saci biliyan hudu, to, a nan da wadannan kudade rijiyar burtsatse nawa za a yi?