Imrana Abdullahi Daga Kaduna
A Jihar Katsina binciken da masana harkokin ma\’adinai suka gudanar ya nuna cewa, akwai kananan hukumomi hudu da ke makare da zinari, wanda dalilin irin al\’barkar da Allah ya ajiye a Jihar a halin yanzu kamfanoni 100 suka nuna sha\’awarsu domin zuba jari a fannoni daban-daban.
Kananan hukumomin sun hada da Safana da Faskari da Sabuwa da kuma Dan Musa kamar yadda masanan da suka gudanar da binkicen suka bayar da tabbacin cewa da akwai dimbin Zinari a wadannan kananan hukumomi abin da kawai ya rage shi ne ayi kokarin fitar da shi domin ciyar da jihar tare da kasa baki daya gaba.
Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya tabbatar wa manema labarai hakan a Katsina, inda ya ci gaba da bayanin cewa domin bayar da kwarin gwiwa ga duk mai son zuba jari a jihar akwai tanajin haraji na tsawon shekaru uku da ba za a biya ba da kuma tanajin samar da ruwa da filin yin aikin noma ko kafa kamfani da tsaro da sauransu ga duk mai sha\’awar zuba jari a jihar.
Ya ce jihar a yanzu haka tana kan gaba wajen samar da tumatiri wanda a kan hakan ne wani kamfanin kasar waje zai kafa kamfanin sarrafa shi a cikin jihar.
Su dai kamfanoni dari da suka bayyana sha\’awarsu za su zuba jarinsu ne wajen bunkasa harkokin noma da ma\’adinai.
binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa a ranar 9 zuwa 11 za a yi wani gagarumin taron zuba jari a jihar da ake sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bude a babban birnin jihar.