Barayin Shinkafa Sun Addabi Manoma A Kebbi

0
1343

Rabo  Haladu  Daga  Kaduna

MANOMAN shinkafa a karamar hukumar Argungu sun wayi gari da wani tashin
hankali, bayan da wasu daga cikinsu suka taras an girbe, tare da sace daukacin
shinkafar da suka noma a bana.
Lamarin dai kamar yadda wani manomi ya shaida wa manema labarai cewa wasu manoman da satar
ba ta fada kansu ba, a yanzu haka sun dukufa wajen gadin gonakinsu a ranar Litinin.
Wasu kuwa tuni suka fara girbe nasu amfanin gonar suna mayarwa gida domin tsoron kara
faruwar hakan.
A cikin watan Nuwambar bara ne shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da
shirin bai wa manoman shinkafa tallafin bashin Naira Biliyan 20 a Jihar Kebbi,
don bunkasa noman shinkafar, aukuwar wannan al\’amari na nuni da cewa, barayi suna son yi wa gwamnatin

tarayya a karkashin shugaba Muhammadu Buhari kafar ungulu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here