Jabiru A Hassan, Daga Kano.
SANYA hannu kan kasafin kudin shekara ta 2016 zai bai wa gwamnatin tarayya damar aiwatar da manufofin ta na ci gaban kasa ta yadda al\’umma za su sami saukin kuncin rayuwa da ake ciki.
Wannan tsokaci ya fito ne daga Alhaji Usman Dan Gwari, wani jigo a harkar hada-hadar kayan gwari da dillancin su, sannan ya nunar da cewa wannan kasafin kudi zai kasance irin sa na farko a kasar nan idan aka dubi irin gwagwarmayar da aka yi kafin ya sami amincewr shugaban kasa.
Haka kuma ya yi fatar cewa za a bude sabon shafi na dangantaka mai kyau tsakanin bangaren zartaswa da kuma majalisa musamman ganin cewa idan akwai fahimtar juna tsakanin wadannan bangarori guda biyu za a sami damar gudanar da ayyuka na alheri ga al\’umma kamar yadda ake ta tsammani.
Daga karshe, Ahaji Usman Dan Gwari ya yi fatar cewa \’yan Nijeriya za su sami ingancin rayuwa idan har suka kara yin hakuri , sannan ya yi fatar Allah ya kara hada kan majalisa da bangaren zartaswa ta yadda aiki zai tafi kamar yadda ake bukata.