Daga Usman Nasidi
WADANSU masu dauke da bindiga sun kashe shanu 83 a kauyen Adayi da ke karamar Hukumar Nasarawa da ke Jihar Nasarawa, yayin da basaraken Loko ya ce an kashe mutum 20 a.’yan makonnin da suka gabata.
Ana zargin kashe-kashen na daukar fansa ne da masu dauke da bindiga da suka tsallako daga Jihar Benuwai suka aiwatar da su.
Sarkin Loko, Alhaji Abubakar Ahmed Sabo ya yi zargin cewa matasan Agatu ake tunanin suka aikata wannan danyen aiki.
Sarkin Loko, Alhaji Abubakar Sabo, ya ce a ’yan makonnin da suka gabata fiye da Fulani maza da mata da yara 20 na al’ummar Fulani ne aka kashe a yayin hare-haren da ake zargin matasan Agatu daga Jihar Benuwai suka kai yankin.
Ya ce yankin Raya kasa na Loko yana da ’yan sanda biyu ne kacal da ba su da bindiga, inda ya yi kiran da a kara yawan jami’an tsaro a yankin.
Sarki Sabo ya bukaci Fulani da kada su ce za su dauki fansa, saboda gwamnati tana duba lamarin rikicin.
Majiyarmu ta ce duk da cewa jami’an tsaro sun fara gudanar da bincike kan hare-haren,jagoran al’ummar Fulani na yankin Loko Mala Bideri Ahmadu ya yi zargin cewa akwai yiwuwar ’yan bindigar da suka aiwatar da kisan sun fito ne daga yankin Agatu da ke Jihar Benuwai ne.
Malam Bideri Ahmadu, wanda ya gana da manema labarai a garin Loko ya yi zargin cewa matasan Agatu sun tsallako daga Jihar Benuwai da misalin karfe 10:30 na dare a ranar Asabar da ta gabata.
Ya ce wadanda ake zargin sun so “Su sace shanu ne a jiragen kwale-kwalensu ta kan Kogin Benuwai, amma sai shanun suka fashe sakamakon karar harbe-harben bindiga, Kuma da suka fahimci ba za su cimma burinsu ba, sai matasan na Agatu suka bude wa shanun wuta suka kashe 83. Wadanda aka raunata su kuma suna can cikin daji.”
Daraktan Harkokin Mulki (DPM) na yankin Malam danlami Umar, ya ce masu gudanar da sana’ar su a yankin suna cikin wahala sakamakon yadda matasan Agatu suka kwace yankin da ke da ruwa kuma suke kashe duk wanda suka ci karo da shi.
Kakakin ’Yan sandan Jihar Nasarawa, Isma’ila Numan ya ce Babban Ofishin ’Yan sanda na Nasarawa ya samu rahoton kashe shanun 83 da wadanda ake zargin suka yi kuma suna kan gudanar da bincike.
Wata majiya mai tushe ta kusa da jami’an tsaro ta ce: “Ana zaman dar-da a yankin tun bayan kashe fiye da al’ummar Agatu 300 a Jihar Benuwai da ake zargin Fulani makiyaya da aikatawa, Kuma muna zargin wannan harin daukar fansa ne daga bangaren matasan Agatu wadanda ba su son Fulani makiyaya su ci gaba da zama a yankin.”
Majiyar ta kara da cewa: “Rikici a tsakanin
Fulani da Agatu yana matukar barazana ka rayuwa da dukiyar jama’ar jihohin biyu, Kuma Gwamnatin Jihar Nasarawa da ta Jihar Benuwai suna ta kokarin shiga tsakani don kawo karshen rikicin Fulani da kabilar Agatu.”