GWAMNATIN APC NA DA KYAKKYAWAR MANUFAR YIN AIKI – KANTOMAN IGABI

  0
  1162
  Daga Usman Nasidi Kaduna

  KANTOMAR Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna Honarabul Jabir Kamis, ya bukaci al\’ummar kasar nan da su kara hakuri domin gwamnatin  na da kyakkyawar manufar  yi wa al\’umma aiki.

  Kontoman ya bayyana hakan ne a wata ziyarar daya kaiwa wata kungiyar Azama da wayar da kan al\’umma wato RAAF da ke garin Rigasa Kaduna a ranar lahadin da ta gabata.

  A jawabin daya gabatar bayan amsa tambayoyin \’ya\’yan kungiyar, Kantoman ya bayyana cewa akwai shirye-shirye da tsare-tsare masu yawa da suka yi don ganin cewa sun kawo cigaba ga al\’ummar karamar hukumar Igabi ga baki daya.

  Yace \” wannan gwamnatin tun daga farkon ta, ta riga tayi tsari wanda za a kawo wa al\’umma cigaba dukda halin da ake ciki na karayar tattalin arzikin kasa, don haka ba za muyi kasa a gwiwa ba da \’dan abinda muke dashi don yiwa jama\’a aiki domin su san gwamnatin tana sane dasu.\”

  Honarabul Kamis ya kara da cewa halin da suka tsinci kansu a ciki yanzu, wani yanayi ne wanda sai sun samu karin kudi kafin su biya albashi, to amma za suyi amfani da \’dan abinda suke dashi don biya wa al\’umma bukatunsu.

  Acewarsa, suna saran za a samu canji na al\’amura daga karshen wannan watan, dukda yake basu fasa cigaba da yin wasu ayyukan alkhairin da suka tarar a kasa ba wadanda magabatansu suka bari don al\’umma su amfana da su.

  A karshe, Kantoman Hinarabul Jabir Kamis ya yi kira ga al\’ummar kasar nan dasu cigaba da yi musu addu\’a na fatan alkhairi don cimma kyakkyawar manufofinsu na kawo dawamammen canji na cigaba ga al\’ummomi da yankunansu baki daya.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here