Takurawar Da Ake Yi Wa Fulani A Nijeriya Ta Yi Yawa -Sale Bayare

    0
    1276

    Isah Ahmed Daga  Jos

    Alhaji Sale Bayari shi ne  sakataren sabuwar kungiyar nan ta  ci gaban
    al\’ummar fulani a Nijeriya [GAFDAN] kuma  tsohon sakataren kungiyar
    fulani  makiyaya ta  miyetti Allah ta Nijeriya.

    A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu kan zarge-zargen da ake yi wa
    al\’ummar fulani kan  tashe-tashen hankula a Nijeriya, ya kare al\’ummar
    fulanin kan wadannan zarge-zarge da ake yi masu, tare da kawo
    shawarwari kan hanyoyin da za a warware wadannan matsaloli.

    Ga yadda tattaunawar ta kasance:

    GTK; Mane ne za ka ce kan zarge-zargen da ake yi wa al\’ummar fulani kan
    kai hare-hare  a Nijeriya?

    Sale Bayari; To, abubuwan da kowa ya sani ne a Nijeriya, cewa  a cikin
    shekaru 16 da suka gabata  na mulkin farar hula. An koma wata irin
    rayuwa ta siyasa wadda wasu suka dauka idan ba su hargitsa al\’amura a
    addinance ko a kabilance ba, ba  za su ci zabe ba. Wannan shi ne ya
    jawo mana rikice-rikice  iri-iri a Nijeriya, musamman a yankin arewa
    ta tsakiya da wasu suke kira Midle Belt.
    A wannan yanki na arewa ta tsakiya aka dauko wani ra\’ayi na kiyayya ga
    al\’ummar hausawa da fulani  aka sanya su a gaba.  Ko ana jihar Filato
    a lokacin da aka yi rikicin Jos na ranar 7 ga watan 9 na shekara ta
    2001, ta\’adin da aka yiwa  al\’ummarmu a irin yankunan  Barikin Ladi
    da Riyom da Jos ta Kudu suna da yawa.
    A lokacin da aka kira mu gaban kwamitin binciken wannan rikici na Mai
    shari\’a Niki Tobi mun kai lissafin mutanen da aka kashe mana a wannan
    rikici na mata da qananan yara. A lokacin ne aka gano cewa a kashi 70
    bisa 100 na mutanen  da aka kashe a wannan rikici mutanenmu ne.
    Ko a farar takardar da tsohon gwamnan jihar Filato Jonah Jang ya fitar
    kan wannan rikici, a shekara ta 2009 ya nuna irin dibbin mutanen da
    aka kashe mana  a wadannan yankuna.
    A lokacin \’yan kudu saboda suna da jaridu sai aka sami hadin kai na
    bangaren qabilanci da bangaren addini, kafin kace haka sai masu neman
    kuri\’a a arewa  suka zo suka hade da wasu mutanen arewa.  Sai ya
    zamanto  a lokacin tun da shugabannin kasar daga kudu suke,  sai suka
    rika amfani da irin wadannan rikice-rikice.  Kowa ya zamanto yana
    amfani da siyasar kabilanci da addini a lokacin don samun biyan
    bukata.
    Duk inda ake zargin fulani da rikice-rikice idan ka duba zaka ga akwai
    kabilanci da addini a ciki. Kuma duk abin da ya faru idan kai  ba
    Bafulatani ne  ko kuma kai Bahaushe ne ba za a ji komai ba. Amma idan
    kai wani yare ne dan arewa ko dan kudu idan wani abu ya same ka,  sai
    ka ji Nijeriya baki daya ta amsa.
    A shekara ta 2013 an kira mu a majalisar wakilai ta tarayyar Nijeriya,
    a inda ake son a yi dokar samun burtali  da makiyaya ga fulani makiyaya
    a Nijeriya. Muka je muka gabatar da dalilan da suka sanya muke sun a
    samar da burtaloli da wuraren kiwo ga fulani makiyaya a Nijeriya.
    Kafin ka ce kwabo sai aka mayar da wannan abu zuwa ga addini haka \’yan
    arewa wadanda ba musulmi ba, da \’yan kudu wadanda ba musulmi ba, suka
    hade aka dakile wannan doka.
    Idan ana son a zauna lafiya kuma dukkanmu mun yarda cewa mu \’yan
    Nijeriya ne, abin da ya sami wani daga cikinmu ko na alheri ko na
    bakin ciki ya shafi kowa daga cikinmu.
    Duk inda ka ji an taba Bafulatani idan ba a mayar da hankali ba. Ko
    bajima ko badade za ka ji wani abu ya faru a wajen. Saboda haka nake
    gaya wa jama\’a cewa idan kun ji Bafulatani ya taba wasu mutane a wani
    waje to a tambaya mutanen nan su fadi gaskiya tsakaninsu da Allah ba su
    yiwa fulanin nan wani abu ba?
    Domin gaskiyar magana idan ka sami fulani sun je sun  taba wasu mutane
    a wani wuri to a binciki wadannan  mutanen su  fadi mene ne suka
    yiwa fulanin? Idan suka ce basu yi masu komai  ba,  to wannan abin da
    aka yi masu ba fulani ba ne, wasu ne daban.
    GTK; Wato a ganinka irin takurawar da ake yi wa fulani a kasar nan  ne
    yake kawo wadannan rikice-rikice da suke faruwa?

    Sale Bayari; Kwarai kuwa domin takurawar da ake yi wa fulani a Nijeriya
    ta kai inda ta kai. Domin akwai takurawar da fulani  suke fuskanta a
    Nijeriya ta irin  yanayin yau akwai kuma takurawa ta muhalli, da Allah
    ya kawo. Wato kamar dumamar yanayi da Allah ya kawo domin a yau duk
    inda ake zaune a duniya za ka ga mutanen da suke zama a arewa suna
    kaura suna suna komawa kudu, saboda ruwa yana da ta barin arewa yana
    komawa kudu.
    Don haka a yau mutanen Nijar babu yadda za a yi su je arewa su ce za su
    yi kiwo, sai dai su taho kudu don kiwo. Haka mutane Chadi da Mali da
    Kamaru duk idan suka tashi kudu suke tahowa. Kuma babu yadda za a yi a
    Nijeriya a ce wani dan Nijeriya ba zai je wani  waje ya zauna ba. A da
    fulanin da suke zaune a  Sakkwato da Zamfara da Katsina da Jigawa da
    dai sauransu ruwan da ke wuraren ya ishe su rani da damina. Amma yanzu
    baki daya wadannan wurare sun bushe saboda canjin yanayi na muhalli.
    Saboda haka manoma yanzu ba sa samun amfanin gona kamar yadda suke samu
    a da.
    Saboda haka babu yadda za a yi makiyayi ya zauna wurin da babu ruwa da
    ciyawa. Kuma a ce bafulatani bai isa ya je kudu ba. duk da cewa duk
    Nijeriya ce. Alhalin suma mutanen kudu suna tashi suna zuwa ko\’ina a
    Nijeriya suna gudanar da harkokinsu. Suna zuwa Maiduguri da Sakkwato
    da Adamawa da Kano suna harkokinsu.

    GTK; Mane ne za ka ce kan umarnin da shugaban kasa Muhammad Buhari ya
    bai wa Babban Sifeto Janar na \’Yan sanda  Nijeriya kan a kamo wadanda
    suka kai hari kwanakin baya a yankin Iyamurai wadanda ake zargin
    fulani ne?

    Sale Bayari; Ni a wurina wannan umarni da shugaban kasa ya bayar ya yi
    daidai. Duk inda dan ta\’adda da mai laifi yake idan aka ce a je a kamo
    shi, wannan ba laifi ba ne. Tun da ba an ce a je a hallaka shi ba ne kamar
    yadda ake yi mana.
    Ana yi mana zargi cewa fulani suna fyade da sata da fashi da barna kan
    wannan sai a je a far masu a kashe su. To  ko da fulani suna fyade da
    fashi da sata kamar yadda kowace al\’umma take yi. Fashi da sata da
    fyade da satar mutane a wajen mutanen kudu aka fara gani a Nijeriya.
    Yanzu a kudu akwai inda ake barbarar \’yaya mata suna haihuwar jarirai
    ana sayarwa kamar yadda ake kiwon kaji.
    Don haka idan shugaban kasa ya ce duk wanda ya yi laifi a kasar nan a
    kama shi, ya yi daidai saboda za  yi bincike ne kafin a kai kotu.
    Sai dai kawai abin da zan fada a nan shi ne a matsayinsa na shugaban
    kasa yana da kyau dama wannan aiki ne na jami\’an tsaro ba sai shugaban
    kasa ya fito ya bada umarnin a je a kama masu laifi  ba.  Idan aka ce
    sai shugaban kasa ya ce a je a kama masu laifi a cikin kashi 100 ba za
    a kama kashi 10 ba.
    Domin shugabannin kasar nan da suka gabata ba su yi haka ba,  tun daga
    lokacin tsohon shugaban kasa Obasanjo har ya zuwa ga tsohon shugaban
    kasa Jonathan ana rikici tsakanin fulani da manoma, amma babu wani da
    ya ce a je a kama manoma ko makiyaya. Mu mun sani an zo ne an uzura
    wa shugaban kasa Buhari, domin ana son a nata shi, saboda ana ganin
    shi Bafulatani ne saboda haka ya kamata ya dauki wannan  mataki a kan
    abin da fulani suke yi. Mu kuma muna ganin abin ba haka yake ba, domin
    duk wani da ya yi laifi a kasar nan shugaban kasa ya wuce ya ce shi ga
    kabilarsa ko ga addininsa, shi shugaban kasa na kowa ne.  Kuma
    hakkinsa ne ya kare kowa a Nijeriya saboda haka muna kira duk inda aka
    taba fulani shugaban kasa ya bada umarnin a je a bincika a kamo wadanda
    suka taba fulanin.  Kuma duk inda ake zargin cewa bafulatani ya je ya
    yi wani abu ya bada umarni kamar yadda ya bada wannan umarnin a je a
    nemo bafulatanin da ya yi wannan laifi a bincika a yi masa hukumci.

    GTK; A kwanakin baya gwamnonin arewa sun fara tattaunawa kan shirin
    killace fulani a wuri daya, don magance wadannan matsaloli. Mane ne
    ra\’ayinka kan wannan al\’amari?

    Sale Bayari; A kullum nakan ce masu wannan magana ta killace fulani
    ba su fahimci mane ne ake nufi da killace fulani ba. Domin na san maganar
    a killace fulani a kasar Amurka aka fara ta, tun a shekara ta 1880,
    amma har yanzu akwai fulani makiyaya da suke yawo a kasar ta Amurka.
    Kuma a duk duniya musamman a nan Afrika  babu inda aka killace fulani
    aka ce dole su zauna a wuri daya. Akwai makiyaya a Afrika ta Kudu
    akwai makiyaya a Afrika ta Tsakiya akwai makiyaya a Afrika ta Yamma,
    amma babu inda aka taba killace fulani a wuri daya aka ce dole su
    zauna a wuri Daya. Saboda haka wannan abu ba zai yiwu ba a Nijeriya.

    GTK; Wadanne hanyoyi ne kake ganin za a bi a warware wadannan matsaloli?

    Sale Bayari; To kamar yadda na gaya maka ne mun yi kamar shekaru 7
    muna kokarin ganin an samarwa da fulani makiyaya a Nijeriya,
    burtaloli da wuraren kiwo. Misali a duk lokacin makiyayi zai tashi
    daga makiyaya ta yankin Wase zai zo makiyaya ta yankin Mangu a jihar
    Filato. Za a iya sanin ya taso ne daga makiyaya ta yankin Wase saboda
    tana karkashin hukuma. Lokacin da ya taso daga yankin Wase za a iya
    gayawa masu kula da makiyaya ta yankin Mangu. In zama zai yi an san da
    shigowarsa da zaman da zai yi, idan zai wuce ne an san inda zai wuce.
    Ka ga kowanne Bafulatanin da yake kiwo an san da zamansa. Wannan shi ne
    zai magance wadannan matsaloli.

    GTK; Karshe wanne sako  ne kake da shi zuwa ga gwamnati dangane da
    wadannan al\’amura na fulani?

    Sale Bayari; Sako na ga gwamnati shi ne ta gaya wa majalisar tarayya
    cewa suna da hakki su tabbatar da kowanne dan Nijeriya yana da kariya.
    Wadannan fulani da ake magana ba su  wasu da wata sana\’a da ta wuce
    kiwon dabbobinsu. Saboda haka a shirye suke su bayar da rayukansu kan
    wadannan dabbobi nasu.  Don haka dole ne a dubi hakkin fulani a kasar
    nan, a daina kyamarsu a ba su ‘yancinsu domin suma  \’yan Nijeriya.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here