Zan Yi Bincike Kan Wutar Lantarki —Buhari

0
1105

Rabo Haladu Daga Kaduna

SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya ce zai binciki gwamnatocin da suka gabata
kan yadda suka tafiyar da harkokin wutar lantarki.
Shugaban ya bayyana haka ne a yayin tattaunawa da manema labarai a Katsina a karshen mako.
Shugaba Buhari ya ce Najeriya ba za ta ci gaba ba idan dai ba a samu tsayayyiyar wutar
lantarki ba, yana mai cewa dole ya yi bincike kan makudan kudaden da gwamnatocin da suka
gabace shi suka kashe a fannin domin yin gyara mai dorewa.
Ya ce, \”Dole ne mu yi bincike kan makudan kudaden da aka kashe a harkar wutar lantarki,
ganin cewa duk da kudin da aka kashe ba a samun isasshiyar wutar. Matsalar ma\’aikatar
samar da hasken lantarki kamar matsalar ma\’aikatar man fetur ce. An kashe fiye da
$16bn amma babu tsayayyiyar wuta.\”
A baya dai tsohon shugaban kasa, marigayi Umaru Musa \’Yar Aduwa ya zargi tsohon
shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo da kashe fiye da $16bn domin samar da wutar
lantarkin amma maimakon hakan kasar ta ci gaba da fama da matsalar rashin wutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here