Jabiru A Hassan, Daga kano.
Wasu fusatattun matasa sun kone gidan sanatan kano ta kudu Alhaji Kabiru Gaya da na dan majalisar wakilai mai wakiltar Gaya Abdullahi Mahmoud saboda kin cika alkawuran da suka daukar masu lokacin yakin neman zabe.
Wakilinmu wanda ya ziyarci karamar hukumar ya ruwaito cewa matasan sun yi wani yunkuri na kone gidan shugaban karamar hukumar ta Gaya, amma jami\’an tsaro suka dakile wannan yukuri, kuma matasan sun sanar da cewa sun dauki wannan mataki ne saboda su nuna fushin su kan halin ko in kula da wakilan guda biyu suke nunawa a karamar hukumar, sannan sun bayyana matakin da cewa shine mafi dacewa.
Wani matashi Abdullahi Garba wanda bai shiga zanga-zangar ba, ya shaidawa Gaskiya Tafi Kwabo cewa yanzu fa kan mutane ya waye, don haka yana da kyau masu rike da madafun iko su rika cika alkawuran da suke yiwa al\’umominsu ko kuma su rika haduwa da fushin matasa kan rashin cika alkawari.
Tuni dai rundunar \’yan sanda ta jihar kano ta dauki matakai na tsaro a yankin.