Ya Nemi Gwamna Ganduje Da Ya Kammala Titin Nan Mai Tsawon Kilomita 5
Jabiru A Hassan, Daga Kano.
AN roki Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje da ya fara kammala ayyukan nan na tituna masu tsawon kilo mita 5 wanda tsohuwar gwamnatin Kwankwaso ta fara amma har ya zuwa wannan lokaci ba a kammala su ba.
Wani matashi Malam Umar Maigata shi ne ya yi wannan rokon , sannan ya nunar da cewa wannan aiki na kilomita 5 yana daukar hankalin al\’ummar Jihar Kano, don haka yana da kyau gwamnati mai ci ta yi kokarin kammala shi kamar yadda manufofin ta suke na kammala ayyukan da ta gada.
Malam Maigata ya bayyana cewa muddin ba a sami kammala wannan aiki ba, ko shakka babu za a gamu da ambaliyar ruwa a wasu kananan hukumomin Jihar Kano idan damina ta sauka, don haka ne ya yi kira ga gwamnati da ta hanzar ta bai wa lyan kwangilolin da suke wadannan ayyuku kudade wadatattu ta yadda za su ci gaba da aikin, inda kuma daga karshe ya jinjina wa Gwamna Ganduje saboda kokarin da gwamnatinsa ke yi na bunkasa Jihar