An Gano Sunayen \’Ya\’ya Da Matan Ma\’aikatan Yobe A Takardun Albashi

0
1385

Imrana Abdullahi Daga Kaduna

GWAMNAN Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya yi kurarin cewa zai tona asirin duk wani ma\’aikacin da ya cusa sunan yayansa da matansa a cikin takardun biyan albashi a Jihar.

Gwamna Gaidam ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bayar da tabbacin cewa zai yi waje da dukkan ma\’aikatan bogi da aka saka a cikin takardun biyan albashin Jihar.

Gaidam, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake rantsar da hukumar kula da ayyukan shari\’a a Jihar inda ya tabbatar da cewa babu makawa zai cire duk sunayen ma\’aikatan bogin da wasu manyan ma\’aikatan kananan hukumomi suka saka a cikin takardun biyan albashi.

Ya ce hakika wasu manyan ma\’aikata a matakan kananan hukumomi sun cusa sunayen matansu da yayansu a takardun biyan albashi don haka duk sai na share su baki daya, saboda hakan yana haifar wa da jama\’a matsaloli kala kala da ke haifar da nakasu.

\”Ina da sunayen manyan ma\’aikatan da suka cusa sunayen matansu da yayansu a takardun biyan kudi kuma sun yi hakan ne ta hanyar saba wa dokar aikin da suke yi a kananan hukumomin da suke don haka ina yin kira a gare su da su hanzarta cire sunayen da gagga wa.

\”Kafin wuri ya kure wa mutum ya dace ya hanzarta aiwatar da aiki bisa gaskiya domin ina shirin bayyana sunayen masu yin hakan ga duniya kowa ya sani\”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here