Rabo Haladu Daga Kaduna
HUKUMAR yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta tsare tsohon ministan ilmi Malam Ibrahim
Shekarau.
A jiya ne dai tsohon gwamnan na jihar Kano ya amsa gayyatar hukumar domin amsa
tambayoyi kan zargin yin amfani da wani kaso na kudi, Naira miliyan 950 da aka karkata
akalarsu wajen yakin neman zaben tsohon shugaba Goodluck Jonathan karo na biyu.
Sai dai mai magana da yawunsa ya shaidawa manema labarai cewa, ya musanta zargin amfana daga
wani kaso na kudin wadanda aka ce an raba a turakarsa.