EFCC Ta Bayar Da Belin Shekarau

  0
  1381

  Imrana Abdullahi Daga Kaduna

  BAYAN share tsawon kwanaki biyu a hannun hukumar da ke yaki da rusa tattalin arziki da kuma cin rashawa wato Efcc a halin yanzu ta bayar da belin tsohon gwamna kuma tsohon ministan Ilimi na Najeriya Ibrahim Shekarau.

  Shi dai Ibrahim Shekarau ya shiga ragar EFCC ne bayan da ya tabbatar wa da duniya cewa hakika an raba makudan kudin da aka karbo daga gwamnatin tarayya ta hanyar da bata dace ba kuma an yi rabon kudin a cikin gidansa.

  Sai dai kamar yadda ya ce shi yana cikin gidan nasa a saman bene ko lekowa wurin da ake rabon kudin bai yi ba daga sama.

  Wani jami\’in hukumar EFCC ya shaida wa majiyarmu cewa sun bayar da belin Shekarau amma bai fadi ko a kan kudi nawa aka bayar da belin ba.

  Sai dai ya ce za su iya neman Shekarau a duk lokacin da bukatar hakan ta taso domin suna nan suna ci gaba da bincike a kan lamarin.

  Shi dai Shekarau a yanzu dan jam\’iyyar PDP ne kuma ya taba yin takarar shugaban kasa a karkashin jam\’iyyar ANPP.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here