Rahotannin Rabo Haladu Da Usman Nasidi
HUKUMAR EFCC ta kama wani tsohon gwamnan jihar Kaduna mai suna Ramalan Muktar Yero da dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar PDP mai suna Salihu Sagir Takai.
Kakakin EFCC, Wilson Uwajuren, ya tabbatar wa da manema labarai cewa hukumar ta kama Yero ne ranar Litinin da daddare, kodayake bai bayyana dalilin da ya sa aka kama shi ba.
Sai dai rahotanni na cewa an kama shi ne saboda zarginsa da hannu a karbar wasu kudi daga
cikin Naira Biliyan 23b da ake zargin tsohuwar ministar mai ta kasar, Diezani Allison-Madueke ta raba wa mutane domin yakin neman zaben Goodluck Jonathan, tsohon shugaban kasa.
An kama Takai da Yero ne a jiya Litinin, 16 ga watan Mayu, bisa zargin su da hannu a kudin yakin neman zabe, inda suka kwana a ofishin hukumar da ke jihar Kano, kamar yadda majiyarmu ta rawaito.
Haka kuma majiyarmu ta gano cewa sakataren jam’iyyar PDP na jihar Kano mai suna Alhaji Auwalu Ibrahim Dambazau, shi ma ya shiga hannun hukumar EFCC.
A yayin da hake jawabi kan lamarin, wani jigon jam’iyyar PDP a jihar Kano, Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana cewa suna kokarin ganin an bada belinsu.
Haka kuma Iliyasu Kwankwaso ya kalubalanci hukumar ta EFCC, inda ya zarge ta da yin zabe a mutanen da take kamawa. Ya kuma yi mamakin yadda ake tuhumar membobin jam’iyyar PDP kadai.
Shi daai tsohon gwamnan makusanci ne ga tsohon mataimakin shugaban kasa Mohammed
Namadi Sambo.