DAGA USMAN NASIDI
WANI matashi mai suna Adamu Magaji Abdullahi, ya kashe mahaifinsa, Malam Abdullahi da mahaifiyarsa Hafsa da kuma ƙannensa mata biyu, Zainab da Aisha ranar Litinin da daddare da misalin sha daya.
Bincike ya nuna cewa ana dab da auren daya daga cikin kannen nasa da ya kashe, domin bai wuce mako daya ba a daura auren.
Wani jami’i mai hudda da jama’ar ‘yan sandan ya kara da cewa matashin ya kashe mutanen ne ta hanyar amfani da shebir, kuma binciken farko ya nuna cewa ya sha kwayar Tiramol ne.
A cewarsa, tuni aka binne mutanen da matashin ya kashe, sannan za a gurfanar da shi a gaban kuliya da zarar an kammala bincike. Tuni dai aka yi jana’izarsu washe gari da misalin karfe tara na safe.
Kakakin rundunar, Mataimakin Sufuritanda Toyin Joshua da wasu mazauna birnin, wadanda suka tattabar wa da wakilinmu aukuwar lamarin.