Akwai Masu Yaudarar Buhari A Cikin Gwamnatinsa-Kwamared Jibril

0
1078
Isah Ahmed Daga Jos

SHUGABAN kungiyar kwadago ta Jihar Filato Kwamared Jibrin Bancir ya
bayyana cewa babu shakka akwai masu yaudarar shugaban kasa Muhammad
Buhari a cikin gwamnatinsa, da suke ba shi shawarwarin da ba na gaskiya
ba.

Kwamared Jibrin Bancir ya bayyana haka ne a lokacin da yake
zantawa da wakilinmu  a Jos, kan yajin aikin da suka shiga kan janye
tallafin mai da gwamnati ta yi.
Ya ce \’\’muna son \’yan Nijeriya su fahimci cewa lokacin da shugaban kasa
Muhammad Buhari yake yakin neman zabe, ya yi alkawarin cewa idan ya ci
zabe zai sayar da litar mai naira 45. Ya ce bayan da ya ci zaben sai
ya ce wannan tallafi da ake bayarwa karya ne babu shi. Amma sai ga shi
abin mamaki  yau an wayi gari ana cewa  an janye tallafin mai a
Nijeriya.
\’\’Kuma a lokacin  takardar da suka nuna mana sun ce ana sayen litar
man fetur daya, kan naira 86.5 kuma  tallafin naira 13.70 ne. Idan ka
dubi wannan tallafi da gwamnati ta yi bayani a lokacin da kuma farashin
man sai ka ga bai kai naira 100 ba, amma sai ga shi gwamnati ta zo ta
mayar da man nan naira 145. Ka ga wannan ya nuna cewa ba maganar
tallafi ake yi ba. Ya kamata idan ma an ce an cire tallafi ne to kada
farashin man ya wuce naira 120. Kuma aka sake ce mana an bai wa \’yan
kasuwa dama su je kasuwar Dala su nema su saya sannan su fita, su je su
sayo man nan. Idan ka dubi yadda farashin Dala yake ta tashi a
Nijeriya, Allah ne kadai ya san yadda \’yan kasuwar nan za su sayar da
mai\’\’.
Kwamared Jibrin ya yi bayanin cewa idan wannan janye tallafin mai ya
tabbata, kudin abinci da  kudin hayar gidaje da kudin shiga mota da
kudin makaranta da kudin asibiti da dukkan wasu abubuwa da jama\’a suke
amfani  da su, za su kara tashi sama.  Saboda haka talakawan Nijeriya
za su shiga cikin mummunar wahala.
Ya ce don haka muka fito muka nuna wa duniya cewa ba mu yarda a danne
mana hakki ba. Domin mun zabi wannan gwamnati ne domin ta kare
hakkinmu.
Ya ce shugaban kasa Buhari ya yarda cewa akwai masu yaudararsa a cikin
gwamnatinsa, da suke son su hada shi da \’yan Nijeriya da suke kaunarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here