PDP Ta Dare Gida Biyu

    0
    1174

    Imrana Abdullahi Daga Kaduna

    A halin yanzu dai jam\’iyyar PDP wato babbar mai adawa a tarayyar Najeriya ta samu kanta cikin wani halin tsaka mai wuya wanda sanadiyyar hakan ta rabe gida biyu.

    Kamar dai yadda aka sani da akwai bangaren shugabanta na riko Sanata Ali Modu Sheriff,sai kuma daya bangaren da ya bayar da sanarwar cewa zai yi taron fitar da sababbin shugabannin PDP a babban birnin tarayya Abuja wato dai bangaren su Furofesa Jerry Gana.

    Yayin da su kuma bangaren Ali Modu suka bayar da sanarwa wanda ya zuwa yanzu ma rahotanni na bayanin cewa an kammala shirin gudanar da taron zaben shugabannin a birnin Fatakwal na Jihar Ribas.

    Shi dai Ali Modu Sheriff wanda tsohon Gwamna ne ya tabbatar da cewa kwamitin amintattun jam\’iyyar ya amince ne a yi babban taron jam\’iyyar a ranar Asabar mai zuwa wato gobe a garin Fatakwal don haka duk wanda ya yi babban taro a wani wuri haramtacce ne.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here