Rabo Haladu Da Imrana Abdullahi Daga Kaduna
MAJALISAR limamai da malaman jahar Kaduna na gudanar da taro ne gabanin fara
Azumin watan Ramadan.
Malaman na magana ne a bisa yadda ya kamata a gudanar da Tafsiri a cikin hikima, haka kuma
Malaman na cewa ya kamata \’yan Kasuwa su rangwanta wa jama\’a don samun sassaucin
kayan masarufi a lokacin Azumi.
Sun kuma duba batutuwa kamar yaki na cin hanci da rashawa, da batun yan
kungiyoyin ta\’adda na yankin Naija Delta wadanda malaman suka ce ya kamata a
fuskance su kamar yadda aka fuskanci Boko Haram.
Batun halin matsin tattalin arzikin da suka ce jama\’a na ciki ya janyo talauci tsakanin al\’uma.
Sun kuma bukaci shugaba Buhari da ya duba batun cire tallafin Mai da gwamnati ta yi sosai,
da kuma yin tankade da rairaya cikin masu ba shi shawara, saboda akwai masu yi masa
zagon kasa.
Malaman ta bakin Malam Yusuf Arrigasiyyu, ya jawo hankalin gwamnati da cewa ya dace su dukufa wajen kokarin bayar da horon bita ga Malamai a madadin kokarin yin dokar da za ta takaita wa masu wa\’azi yanayin aikinsu na fadakarwa.
Taron dai ya samu halartar dimbin Malamai da Limamai an kuma yi taron ne a dakin taro na gidan tunawa da Sardauna da ke Kaduna.
Sun kuma bayar da goyon bayan a rika tace duk wani wa\’azi kafin a yada shi a kafafen yada Labarai domin samun zaman Lafiya a tsakanin masu wa\’azi da kuma gwamnati da sauran jama\’ar gari baki daya.