Daukacin Ma\’aikatan Jihar Bauci Sun Yi Zanga-zanga

0
1156

Imrana Abdullahi Daga Kaduna

SAKAMAKON kwashe watanni akalla biyar da ma\’aikatan Jihar Bauci suka yi ba tare da biyansu albashi ba ya sa ma\’aikatana suka fantsama kan titunan babban birnin jihar inda suka yi zanga-zangar kin amincewa da halin da suka shiga.

Su dai ma\’aikatan sun zargi gwamnatin Jihar Bauci ne da jefa su cikin matsalar rashin biyan albashi har tsawon watanni biyar.

Ma\’aikatan da suka fito su dubbai sun bayyana wa duniya irin matsalar da suke ciki su da iyalansu inda wata mata ta bayyana cewa ta kasa biya wa danta kudin rubuta jarabawar fita makarantar sakandare sakamakon rashin albashi.

Wannan takaddama dai ta taso ne bayan da gwamnatin Jihar Bauci ta fara kokarin ci gaba da aiwatar da aikin tantance ma\’aikatan ban da wadanda aka yi a can baya, nan fa sai suka fara tururuwa daga garuruwa daban-daban na jihar suna shiga babban birninsu domin aiwatar zanga-zanga a kan tituna

Sai dai gwamnatin jihar ta saurare su inda suka tabbatar masu cewa an janye batun ci gaba da tantance ma\’aikata kuma nan da kafin Azumi za a yi kokarin biyansu albashi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here