Imrana Abdullahi Daga Kaduna
A kokarin ganin an magance matsalolin da suka taso wa jam\’iyyar PDP har take neman wargajewa , an nada tsohon gwamnan Kaduna Sanata Ahmed Muhammad Makarfi a matsayin sabon shugaban jam\’iyyar.
An kuma nada tsohon gwamna Peter Obi a matsayin sakataren PDP da za su yi aiki na tsawon watanni uku kafin a zabi sababbin shugabanni.
Abin jira a gani shi ne yadda sauran \’ya\’yan jam\’iyyar da ke taro a birnin Fatakwal za su mayar da martani a kan wannan batu.