Duk wanda ya yi karatun kiwon lafiya zai taimaki al\’umma-Sheikh Jingir

0
1906

Isah Ahmed Daga Jos 

SHUGABAN majalisar malamai na kungiyar Jama\’atu Izalatil Bid\’ah  Wa\’ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh  Muhammad Sani Yahya Jingir, ya
bayyana cewa duk wanda ya yi karatun kiwon lafiya zai taimaki al\’umma,
musamman mata da suka karanci kiwon lafiya. Sheikh Muhammad Sani
Yahya Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron
bude makarantar kiwon lafiya ta Sahlan da ke garin Jos a ranar lahadin
da ta gabata.

Ya ce wannan makarantar kiwon lafiya ta Sahlan da aka bude tazo a
daidai lokacin da ake bukatarta don haka samuwar wannan makaranta wani
babban abin farin ciki ne.

Ya yi  kira ga gwamnatin jihar Filato ta taimakawa   wannan makaranta,
ta hanyar daukar nauyin biyan albashin wasu malaman makarantar, domin
makarantar zata taimakawa gwamnatin jihar kan harkokin kiwon lafiya.

Sheikh Sani Yahya Jingir wanda mataimakinsa na biyu Sheikh Sa\’idu
Hassan Jingir ya wakilta, ya yi kira ga daliban  makaranta su   tsaya
su  yi karatu tsakani da Allah domin su zo su taimaki al\’umma.

Har\’ila ya yi kira ga malaman wannan makaranta  su zamanto babu sani
babu sabo tsakaninsu da kowanne dalibin wannan makaranta kan harkokin
karatu.

Ya ce domin idan aka bari aka yi satar jarrabawa a wannan makaranta,
za a iya  jefa al\’umma a cikin mummunan hadari,  domin wannan fanni ya
shafi  lafiya da rayuwar al\’umma  ne gabaki daya.

A nasa jawabin gwamnan jihar Filato  Simon Bako Lalong ya bada
tabbacin cewa gwamnatin jihar zata  tallafawa makarantun kiwon lafiya
masu zaman kansu da ke jihar, don karfafa masu gwiwa wajen horar  da
nagartattun  jami\’an kiwon a jihar.

Ya ce gwamnatin jihar zata tallafawa irin wadannan makarantun ne,
ganin irin   taimakawa gwamnatin  jihar da suke yi  wajen  sauke
nauyin da ke kanta, na kiwon lafiyar al\’ummar jihar. Don haka ya ce
gwamnati  zata taimakawa wannan makaranta ta Sahlan, da  sauran irin
wadannan  makarantu  da ke jihar.

Gwamnan ya ce sai dai gwamnatin jihar  ba zata amince a rika yaye
daliban da basu cancanta ba a irin  waxannan makarantu. Ya ce don haka
dole ne ma\’aikatar kiwon lafiya ta jihar, ta sanya idanu wajen ganin
ana bin ka\’idoji a irin wadannan makarantu.

Gwamnan wanda mataimakin shugaban ma\’aikatan gidan gwamnatin jihar
Filato Barista Yusuf Gambo Hawaja ya wakilta, ya yi bayanin cewa
dukkan asibitoci  da ake da su  a jihar,  ba zasu iya gudanar da
ayyukansu ba idan babu irin waxannan makarantu. Don haka ya yi kira ga
jami\’an irin wadannan  makarantu  su yi koqari su horar  da ma\’aikatan
kiwon lafiya na gari wadanda zasu taimakawa al\’umma wajen kiwon
lafiya.

Tun da farko a nasa jawabin Daraktan Makaranta kiwon lafiya ta Sahlan
Malam Muhammad Shafi\’u Yakubu ya bayyana cewa sun kafa wannan
makaranta ne, tare da hadin gwiwar shugaban kamfanin mai na A.A Rano
Alhaji Auwal Abdullahi.

Ya ce manufar kafa wannan makaranta shi ne domin su samar da wata
babbar cibiya wadda zata   bayar da gudunmawa kan harkokin kiwon
lafiya a Nijeriya da duniya gabaki daya.

Ya ce a kokarinsu na ganin sun cimma wannan manufa, sun yi bincike
tare da neman shawarwarin qwararru kan harkokin kiwon lafiya kan
dukkan abubuwan da ake bukata a wannan makaranta.

Ya ce sun samar da azuzuwa da ofisoshin malamai da dakunan bincike da
dakin karatu da dakin na\’urar kwanfuta da dakin taro da motar daukar
dalibai da dai sauransu. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here