Imrana Abdullahi Daga Kaduna
Labaran da ke fitowa daga Jihar Legas na cewa wata kotu karkashin mai shari\’a Ibrahim Buba, ta sauke Sanata Ahmad Muhammad Makarfi, daga shugabancin PDP da aka nada shi a wajen babban taronsu na kasa a Fatakwal babban birnin Jihar Ribas.
In dai za a iya tunawa dai PDP tuni ta rigaya ta dare gida uku akwai bangarori biyu da Sanata Nasiru Ibrahim Mantu yake wa shugabanci da suka yi taro a Abuja sai kuma na shugaban rikon da aka nada domin ya cike lokacin Ahmad Adamu Mu\’azu da shima ya samu aka nada shi domin cike lokacin Bamanga Tukur don haka lokaci ne kawai zai ba yan Najeriya da duniya baki daya damar ganin abin da zai faru.
Sai dai baki dayan dukkan Lauyoyin da suka halarci kotun nan sun yi ikirarin cewa sun je ne domin kare PDP.
Tun farko dai mai shari\’a Buba ya bayyana cewa kotun tasa ta bayar da umarnin cewa kada ayi zaben shugaba da wasu ofisoshin PDP na kasa har sai ta yanke hukuncin karar da aka kawo mata don haka ta yanke wannan hukunci.
Su kuma gwamnonin PDP sun bayyana cewa ba fa zabe suka yi ba rikon shugabanci kawai aka bayar na watanni uku amma ba zabe ba.