Rabo Haladu Daga Kaduna
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin
arzikin kasa zagon-kasa, EFCC ta ce ta
gano ma\’aikatan gwamnatin tarayya na
bogi su dubu 37, 395.
Shugaban hukumar Ibrahim Magu ya ce sun
gano wadannan mutanen ne a wani aikin hadin
gwiwa da ma\’aikatar kudi da kuma ofishin
babban Akawun gwamnatin tarayya, yana mai
cewa hakan ya sa gwamnatin tarayya ta yi
asarar kusan Naira biliyan daya.
A cewar hukumar, za a ci gaba da gano
ma\’aikatan bogi a yayin da suke ci gaba da
bincike a rijistar albashin ma\’aikatun
gwamnatin tarayya.
A baya dai, ministar kudi, Kemi Adeosun, ta ce
an gano dubban ma\’aikatan bogi a kasar nan wanda haka yasa kudadan gwamnati suke zurarewa zuwa aljihun wasu mutane azalumai.