Imrana Abdullahi Daga Kaduna Najeriya
A bisa bayanan da ke fitowa daga kasar Saudiyya kuma daga bakin mahukuntan kasar sun bayyana cewa Iran taki sa hannu a bisa dokar hana yin Zanga Zanga a kasa mai tsarki.
In dai za a iya tuna wa a lokacin aikin Hajjin bara wani al\’amari ya faru inda aka rasa rayukan jama\’ a da dama sakamakon turmutsutsun mutanen da aka samu lokacin aikin Hajji da ya gabata.
Wannan lamari ne yasa wasu kasashe suka yanke hukuncin yin Zanga zanga a kan mutanensu da suka salwanta a yanayin.
Kamar yadda wadanda ke bayani a kan al\’amuran yau da kullum suke ganin shi yasa kasar Saudiyya ta yi kokarin fitar da ka\’idojin da kasashen duniya za su amince da su Karin lokacin aikin Hajjin bana.
Ita dai kasar Iran ta bayyana wa duniya cewa a bana ba za ta je aikin Hajji ba lamarin da kasar Saudiyya ta bakin jami\’anta suke cewa Iran taki sa hannu a dokar hana zanga zanga a kasarta.
Fata dai a samu dai daito a tsakanin kasashen kafin lokacin aikin Hajjin bana domin ba yan kasar Iran damar sauke farali.