AN BUKACI GWAMNA FAYOSE DA YA BA ‘YAN AREWA HAKURI

0
1428

DAGA USMAN NASIDI

WATA kungiyar North East Youth Peace Development and Empowerment Initiative (NEYPDEI), sun yi kira ga Ayodele Fayose, Gwamnan jihar Ekiti da ya bada hakuri bisa ga furucin da ya yi a kan batan yan matan Chibok.
Fayose yace anyi anfani da batan yan matan Chibok ne domin a sauke tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan daga kan kujerar mulki ta ko wani hali.
Shugaban kungiyar NEYPDI, Alhaji Kyari Idris Abubakar, ya yaba wa kokarin Sojoji da suka
ceto rayuwar Amina Ali, daya daga cikin ‘yan matan Chibok da aka sace.
Abubakar ya soki furucin da Gwamna Fayoshe ya yi na hada rayuwar mutane da
siyasa.a cewar shi, “muna rokon ‘yan Nijeriya da kada su dauki furucin da
Fayose ya yi da mahimmanci domin ba gaskiya ba ne.”
Abubakar ya shawarci Fayose da ya yi mulkin adalci ga mutanen jihar Ekiti, maimakon yin furucin da zai kawo rabuwar kan ‘yan Nijeriya. Idan aka kwatanta halin da iyayen ‘yan matan Chibok suke ciki da zafi. Shugaban kungiyar NEYPDI ya bayyana cewa ba su tsanmaci furuci da zai dada munana zukatansu ba.
“Mun san yawan iyaye nawa ne suka rasa rayukansu daga 14 ga watan Afrilu, 2014,
lokacin da aka sace yan matan, da wani zai zo daga wani wuri yace karya ne babu ko
wacce yarinya da aka sace”, ya bayyana cewa.
A halin da ake ciki kungiyar Boko Haram sun yarda cewa za su ajiye makamansu tare
da sakin sauran matan da suka rage ba tare da sun kisa ko cin zarafi ba.
Amir Muhammad Abdullahi, babban dan kungiyar Boko Haram ya ce: “Muna so mu
ajiye makaman yakinmu domin abubuwa na dada tabbarbarewa.”
Ya kuma ce babu wanda ya samu nasara tsakanin ‘yan ta;addan da sojojin Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here