DAGA USMAN NASIDI
GWAMNATIN Jihar Kogi ta kori shugaban kungiyar kwadago ta jihar Onuh Edoka a kan cewa shi ma’aikacin bogi ne a jihar.
Binciken rahotanni ya nuna cewa Onuh tare da wasu ma’aikatan jihar 9000 an kore su daga aiki a jihar bayan da aka gudanar da tantancewa a jihar.
Edoko wanda shi ne shugaban kungiyar ma’aikatan lafiya na jihar kuma shugaban kungiyar kwadagon jihar an dauki shi aiki ne a shekarar 1989 a matsayin mai zuwa duba cutuka da kuma zagaye a jihar.
Edoko ya bayyana cewa abin ya ba shi mamaki a kan yadda aka gudanar da binciken wanda wani tsohon Janar, paul Okintumo ya shugabanta.
Kwamitin tantancewar ya nemi ya kawo takardar Akawunt din banciken shi wanda ya bayyana cewa ya ba su har na tsawon shekaru 2.
“Kungiyar kwadagon ta tabbatar da cewa wadanda aka kora ma’aikata ne kuma a shirye muke da mu fito mu kungiyar kwadon mu yi zanga-zanga tare dasu.
Amma daga sashen Gwamnatin, maitaimakin Gwamnan Jihar Bello, Gbenga Olorunpomi, ya bayyana cewa an yi adalci a wurin tantance ma’aikatan.
Ya ce ” Gwamna ya yi tsammanin cewa akwai wasu wadanda ma’aikatan bogi ne wadanda suka shigo aiki a haramtacciyar hanya don haka za a kore su. Babu tausayi a kan su.