An Kama Mutane Takwas Masu Fasa Bututun Mai

0
1317

Imrana Abdullahi Daga Kaduna

\”KAMAR dai yadda masu iya magana ke cewa karshen alewa kasa\” wato dai kamar yadda wadansu mutane daga yankin Neja-Delta suke fadin cewa ko ta halin kaka sai sun kassara tattalin arzikin Najeriya.

Sai dai ga shi duk da irin kokarin kiraye-kirayen da mutanen kirki masu son ganin kasar nan ta samu nasarar ci gaban kasa da kowa ke bukata a kasarsa, amma wasu domin kawai suna ganin ana samun mai a yankinsu sai suka mayar da lamarin tamkar na dibar ganima.

Hakan ya sa suke ta satar danyen mai har wasu a cikinsu suka mayar da shi tamkar sana\’a, lamarin da ake gani ko dai da masu daure masu gindi ne?

A cewar kakakin rundunar sojojin Ruwan Najeriya kamar yadda aka bayyana Cer Ezekobe, ya tabbatar da cewa rundunar ta kame mutane takwas da ake zargi da wannan aikin.

An kuma kama wadansu \’yan kasar Benin da jarkokin mai 900 wanda  dama can ana zargin mutanen kasashen waje da aikata wannan aikin kuma duk wanda aka kama za a gurfanar da shi ko su nawa ne a gaban kuliya domin yi masu hukunci.

An dai samu rahotannin da ke cewa a karamar hukumar  Peteta Burutu an sami irin wadannan rahotannin.

Amma su irin wadancan mutane masu cewa a bar masu arzikinsu wasunsu ba sa son fadiwa na kasa kasa gaskiya a kan irin yadda aka bunkasa tattalin arzikin Najeriya da arzikin noman gyada, auduga da sauran abubuwan kayan gona tun kafin a sami abin da ake kira man Fetur a tarayyar Najeriya.

Ku tara a nan gaba kadan za mu kawo maku irin yadda Arewacin Najeriya ke taimakon kudu maso kudu da maso gabas da jakuna, shanu, awaki, tumakai maza da mata da suke ci a gidajensu da dai sauran nau\’in abinci da sauran kayan gudanar da kasuwanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here