Gwamnatin Tarayya Ta Sami Naira Biliyan 50 Dalilin Bankado Ma\’aikatan Bogi

0
988

Rabo Haladu Daga  Kaduna

GWAMNATIN tarayya ta ce ya zuwa yanzu, ta bankado ma\’aikatan bogi dubu 43,000 a
tsarin biyan albashinta da take gudanarwa.
Shugaban kwamitin da gwamnatin ta kafa domin bincike a kan albashin ma\’aikata,
Muhammad Kyari Dikwa, ne ya bayyana hakan.
Ya ce binciken ya kai ga samun rarar kudi na Naira Biliyan 50 a asusun gwamnati.
Hakazalika gwamnati ta ce ba gudu ba ja da baya a kan yaki da cin hanci da rashawa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here