SHUGABAN KASA BUHARI YA BAYYANA NASARORIN DA GWAMNATIN SHI TA SAMU

0
1675

DAGA USMAN NASIDI

SHUGABAN kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana nasarorin da gwamnatin shi ta samu a cikin shekara 1 da kafa ta. Inda ya maganta daga sha’anin tsaro zuwa yaki da rashawa, wutar lantarki da sauran su.
Shugaba Buhari ya bayyana cewa sojojin Najeriya sun ceci sama da mutane 11,595 daga lokacin da ya hau mulki zuwa yanzu kuma sojojin sun amshe duka garuruwan da ke a hannun yan kungiyar kafin ya hau mulki.
Wannan sakon ya fito ne daga Ofishin jami’i mai taimaka ma shugaban kasa Buhari a kan hulda da jama’a, inda ya saki wasu takardu masu suna “Fact sheet on President Muhammadu Buhari’s first year in office”, zuwa wajen yan jarida domin sanar da bayanai a kan cika shugaban kasa Buhari shekara 1 a kan mulki.
Takardun sun yi bayanai ne a kan fannonin tattalin arziki, tsaro, wutar lantarki da yaki da rashawa da sauran su.
Ya ce “Dauke cigabar shiri na soji daga Abuja zuwa Arewa maso Gabas ya taimaka sosai wajen yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram
“A watan Fabrairu, sojojin Najeriya sun ceci mutane 11,595 daga hannunn ‘yan kungiyar.
” Daga watan Disamba sojojin Najeriya suka amso duka hannun ‘yan kungiyar Boko Haram.
Takardun suka ce ” A watan Maris Gwamnatin Najeriya da ta kasar Swiss suka sanya wa yarjejeniya hannu inda suka amince da cewa za a maido da sama da Dala Miliyan 321 wadanda Abacha ya sace kuma suke cikin Bankunan kasar.
” A watan Maris shugaban kasar ya kafa kwamitin bincike a kan Ofishin tsohon mai ba shugaban kasa Jonathan shawara a kan tsaro inda daga hannun shi da kuma kamfanonin da aka ba kudaden aka samo Naira Biliyan 7.
A kan tattalin arziki. sun bayyana cewa Buhari ya kawo Asusun bai daya wanda ya taimaka wajen hana satar kudaden gwamnati kana sun ayyana cewa a da kamfanin Mai na NNPC yana da sama da Akawunt 40, amma yanzu duka an kulle su domin tabbatar da adalci.
Ya bayyana cewa shugaban kasa ya bada umurni ga babban bankin Najeriya da ya saki Naira Biliyan 689.5 domin a fidda jihohi 27 da suke cikin matsi domin su samu biyan ma’aikatan su kana ta bayyana cewa gwamnati ta gano ma’aikatan bogi sama da 34,000 inda hakan ya rage baraka a cikin kasa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here