An Mikawa Sanata Makarfi Ragamar PDP

    0
    1322

    Imrana Abdullahi Daga Kaduna

    A wani kwarya kwaryan taron masu ruwa da tsaki Na yayan Jam\’iyyar PDP da ya gudana a babban sakatariyar ta kasa inda a taron ne aka mikawa tsohon gwamnan Jihar Kaduna sanata Ahmad Muhammad MAKARFI ikon tafiyar da dukkan al\’amuran PDP Na kasa baki daya har zuwa lokacin da za a yi babban zaben shugabannin Na kasa.

    A wajen taron tsohon shugaban riko Na kasa Mista Uche Sokondus, ya shaidawa jama\’ar da suka taru cewa daga yau ya MIKA dukkan al\’amuran tafiyar da jam\’iyyar ga shugabancin rikon da zai shirya sabon zabe.

    Ya kuma CE ya MIKA wannan shugabanci ne ga Sanata Ahmad Muhammad MAKARFI,Wanda shi ne zai ja ragamar komai har a shirya sabon zabe Na kasa.

    Da yake tofa albarkacin bakinsa shugaban kwamitin amintattun PDP Na kasa Alhaji Walid Jibril, bayyana gamsuwarsa ya yi da rikon da aka ba MAKARFI inda ya CE lallai PDP ta dace da shugabanci a yanzu.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here