Gwamnati Ta Kafa Kwamitin Bunƙasa Noman Shinkafa A Nijeriya

0
8706

Rabo Haladu Daga Kaduna

GWAMNATIN tarayya  ta kafa kwamiti na musamman don bunkasa noman shinkafa da
alkama a kasar nan.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo shi ne ya kaddamar da kwamitin
karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Kebbi Atiku Bagudu .
Mista Osinbajo ya sake jaddada aniyar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari wajen
ganin kasar ta dogara da kanta musamman a harkar noman shinkafa da kuma alkama.
Ya ce burin gwamnati shi ne noman shinkafa da alkama ya bunkasa nan da shekara guda.
A karshe ya yi kira ga manoma da su dukufa sosai a wannan damina  ta bana domin raba kasar nan da yunwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here