Ya Dace IBB Ya Rubuta Tarihin Rayuwarsa – Sarkin Birnin Gwari

0
3763

IMRANA ABDULLAHI Daga Kaduna

MAI Martaba Sarkin Birnin Gwari Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari na Biyu, ya fito fili ya bayyana cewa lallai yana da kyau ga tsohon shugaban kasa da ya yi mulki a zamanin Soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya kokarta domin rubuta tarihinsa.

Sarkin Birnin Gwari ya bayyana hakan ne a wajen wani babban taron da aka yi domin kaddamar da littafin da dan jarida Dickson Salami Adama, ya wallafa mai sunan tarihin magabata da aka kaddamar a garin Kaduna.

Ya kara da cewa lokaci ya yi da IBB zai yi kokarin rubuta tarihinsa domin jama\’ar da ke zuwa a nan gaba su samu damar sanin tarihin mutum kamarsa.

\”Musamman idan aka yi la\’akari da irin yadda wadansu mawakan da suka fito daga wani yanki na kasar nan suke ta rera wakoki a kansa\”.

Sai ya yi kira ga daukacin matakan gwamnati uku na Najeriya da su hanzarta lalubo hanyaoyin da za su horar da yara yin karance karance da rubuce rubuce domin muhimmancin abin.

Ya kuma jaddada cewa kokarin rubuta wannan Littafi da matashi Dickson ya yi kalubale ne ga tsofaffi, wanda sakamakon haka ne yasa har yaga dacewarsa da ya halarci wannan taron kaddamar da littafi da yake wa shugabanci.

Da yake tofa albarkacin bakinsa marubucin littafin Dickson Salami Adama,cewa ya yi shekarunsa 6 yana kokarin ganin ya wallafa shi abin da har sai da ya kawo masa kamuwa da ciwon gyambon ciki amma duk da haka sai da ya ga mafarkinsa ya zama gaskiya kuma yana da sauran wadansu Littattafai guda 3 suna nan yana yin aiki a kansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here