Tunawa Da Editan Gaskiya Ta Fi Kwabo Dokta Abubakar Imam

0
1557

Gudunmawa Daga Zubair A Sada GTK

KOWACE shekara dabi\’ar wannan jarida mai farin jini da albarka ce ta tura wakilanta su zagaya wajen dangi da \’yan uwa da abokan arziki domin su kalato mata wasu bayanai dangane da Editan jaridar na farko, wato Marigayi Dokta Abubakar Imam wanda Allah ya yi wa rasuwa ran 19 ga watan Yuni, 1981 a babbar asibitin koyarwa ta Jami\’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

A wancan karo da aka bayyana rasuwarsa, Alhaji Abubakar Imam ya rasu ne yana da shekaru 70 daidai a diniya. Ya zama Editan jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ne a shekarar 1939, kuma a cikin shekarun ne suka yi ta aika wa da sakonnin jaridar musamman ga sojojin kasar Najeriya da suke yaki a kasar Bama,

Marigayi Abubakar Imam, dan baiwa ne domin shi ne irinsa na farko a zamaninsa da ya hada malanta ta darussan harsuna uku, masanin harsunan Arabiyya da Ingilishi da Hausa, domin kuwa ba ka samun fassararsa a cikin wadannan harsuna da gyare-gyare saboda baiwar da Allah ya yi masa.

Shi ne mawallafin fitaccen littafin nan na Hausa, \’Magana Jari Ce\’, wanda ya rubuta littattafai har sufuli uku na \’Magana Jari Ce\’. Haka nan shi ne wanda ya rubuta littafin \’Ruwan Bagaja\’ da sauransu da dama. Marigayin ya yi ayyukan gwamnati daban-daban tare da yin wakilcin Arewa ko kasa baki daya a tarurruka da yawan gaske.

Domin a dinga tunawa da shi, kamfanin buga jaridun NNN da GTK a ginin su na farko sun sanya sunansa ne, ana kiran ginin da suna \’Gidan Imam\’, wato \’Imam House\’, mu kuma a bangarenmu da ya yi wa jaridar da muke aiki cikinta Edita na farko, muna bibiyar ayyukansa da dabi\’unsa da zamantakewarsa da abubuwan da ya bari a doron kasar nan domin a tuna da shi a yi masa addu\’a. Muna kara yi masa addu\’a Allah ya jikansa ya dawwamar da shi cikin rahamarSa, amin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here