WASU DALIBAI SUN KASHE ABOKIN KARATUNSU A KANO

0
1153

Daga Usman Nasidi

WASU dalibai da ba a tantance ko su wane ne ba a makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati da ke garin Gaya a Jihar Kano, sun kashe wani dan uwansu dalibi da ke shekarar karshe mai suna Abubakar Abdullahi.
Bincike ya tabbatar da cewa a ranar Laraba 8 ga Yuni ne rikici ya barke a tsakanin daliban aji uku da na aji biyu na babbar sakandaren lamarin da ya jawo dalibi Abubakar Abullahi ya samu raunka daga bisani rai ya yi halinsa a Asibitin Muhammad Abdullahi Wase da ke Kano.
Mahaifin dalibin Alhaji Abdullahi Muhammad Danladi ya shaida wa wakilinmu cewa, “A ranar da ’yan aji shida suka kammala rubuta jarrabawar su sai yarona ya tafi debo ruwa a rijiyar burtsatse a makarantar, a nan ne wadansu dalibai suka yi masa dukan kawo wuka, wani a cikinsu ya kwada masa dutse a kai.
Ganin raunikan da ya samu ga jini na fita ta hanci da bakinsa ya sa hukumar makarantar ta kai shi Asibitin Gaya. Sai shugaban makarantar ya yi wa dan uwana waya cewa mu zo mu dauki yaron a asibitin Gaya ba ya da lafiya. ’Yan uwana suka je Gaya suka dauko shi suka kai shi Asibitin Muhammad Abdullahi Wase aka kwantar da shi a daki na musamman, kuma saboda jikinsa ya yi tsanani sai aka mayar da mu Asibitin Malam Aminu Kano, a nan ne aka yi hoto aka gano kwakwalwarsa ta tsage.
Ana cikin haka ne sai aka ce likitoci masu neman kwarewa za su shiga yajin aiki, sai muka mayar da shi Asibitin Abdullahi Wase ya rasu a ranar Asabar,” inji shi.
Alhaji Abdullahi ya koka da halin ko-in-kula da Shugaban Makarantar Sakandaren ta Gaya ya nuna a kan lamarin, ya ce tunda aka taho da yaron Kano bai zo ya yi musu bayanin abin da ya same shi ba, kuma bai zo ya duba shi ba.
Ya ce ba ya ga daliban da suka doki yaron yana zargin akwai sa hannun wasu daga cikin malaman makarantar da kisan dansa. Sai ya roki Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kwato masa hakkinsa dansa.
Hakazalika, bincike ya tabbatar da cewa Shugaban Hukumar Kula da Makarantun Kimiyya a Jihar Kano da wasu manyan daraktocin hukumar sun je sun duba marigayi Abubakar a lokacin da yake kwance a asibiti, Kuma hukumar ta yi kokarin biyan kudin jinyarsa.
Shugaban Hukumar Ahmed Tijjani Abdullahi ya bayyana lamarin da abin takaiici, inda ya ce “Mun yi duk abin da za mu iya a hukumance wajan ganin marigayin ya samu kular da yake bukata a asibiti.” Alhaji Tijjani ya tabbatar da cewa rikicin ya faru ne a tsakanin daliban aji uku da na aji biyu na bababr sakandaren makarantar, wanda hakan ya jawo dalibai bakwai suka samu raunuka, shi kuma ya rasu.
Shugaban ya ce hukumar ta karbi rahoton lamarin daga shugaban makarantar, sai dai ba ta gamsu da rahoton ba, don haka ta kafa wani kwamiti bincike na mutum tara mai mutane tara ya sake bincike a kan lamarin tare da mika rahotonsa cikin mako daya, Kuma tuni ta dawo da shugabannin makarantar zuwa hedikwatar ta har zuwa lokacin da za a kammala binciken.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here