Daga Usman Nasidi
KUNGIYOYIN \’yan daba biyu masu adawa sun tayar da tarzoma a garin Omoku a wani yakin bata-kashi da ya faru tsakanin kungiyoyin \’yan daban biyu a garin Omoku,headkwatar karamar hukuman Ogba /Egbema /ndoni ta Jihar Ribas a kudancin Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa tashin tashinan ya faru ne a makon daya gabata, kuma a lokacin anyi garkuwa da mutane guda biyu, daya daga iki wani shahrarren likita ne a unguwar mai sun Dokta Erike.
An bada rahoton cewa kungiyoyin yan daban guda 2 masu suna ‘Icelander’ da ‘ Greenlanders’ sun dade suna adawa da juna,wanda hakan ya ja hasaran rayuka da dama.
\’Yan kungiyar ‘greenlanders’ ne suka kai farmaki unguwar wanda aka rasa rayuka 11 a daren ranan laraba.
Wani mazauni unguwar,Mista Micheal ya fada wa manema labarai cewa yan daban sun shigo unguwan ne suna harbin kan mai uwa da wabi. Ya ce mutane da yawa sun ji rauni harda mai bawa shugaban karamar hukumar shawara akan al’amuran matasa, Mista Smart Igwe.
Ya kara da cewa sun shigo Omoku sun kasha mutane 4 kuma sun yi garkuwa da mutane 2, sannan suka karasa Unguwar Obigwe suka kashe mutane 3.
Hayaniyar ba ta kare ba a jiyan,sun sake dawowa da safe garin Omoku sun kashe mutane 4.
Mista Isaac Umejuru wanda shi ne shugaban karaman hukumar ya nuna bacin ran sa da abin takaicin da ya faru.
Kakakin ofishin yan sanda na Jihar Ribas, Ahmad Muhammad ya bada rahoton cewa kungiyoyin adawa ne suke yakan juna kuma an kasha uku a take.
A wani labara mai kama da hakan, rundunanr Sojojin Najeriya sun kashe yan daba 5 a sakamakon wani musanyan wuta da sukayi a ranar lahadi 12 ga watan yuni.
An bada rahoton cewa yan daban yan kungiyan ‘Icelander’ ne a karamar hukumar Emohua ta Jihar Ribas, Sakomakon bata-kashin, mutane 5 da yan daban sukayi garkuwa dasu a ranar Juma’a a garin elele ta karamar hukumar Ikwerre suka samu \’yanci.