An Bukaci Matasa Su Daina Hada Kai Da Batagari

0
1345

IMRANA ABDULLAHI Daga Kaduna

MINISTAN kula da harkokin matasa da wasanni na tarayyar Najeriya Barista Solomon Dalung ya yi kira ga daukacin matasan Najeriya da su daina amincewa da duk wani mutum da zai yi masu koyarwar da ta sabawa tsarin ciyar da kasa gaba.

Minstan ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya kaiwa shahararren Malamin adddinin Musulunci Shaikh Dahiru USMAN Bauci ziyara a gidansa da ke Kaduna.

Minista Solomon ya CE kamar yadda koyarwar addinin Islama da na Kiristanci suka koyar da jama\’a babu inda aka ga akwai sabani tsakanin bangarorin biyu, don haka duk wanda yake kokarin koyawa matasa wani tsari domin tayar da fitina ya zama dole su gujewa wannan mutum ta yadda za su tsira da daraja da kuma martabar kasa baki daya.

Tun da farko da yake tofa albarkacin bakinsa mai masaukin baki Shaikh Dahiru Usman Bauci, cewa ya yi mai addinin tausayi da mai addinin taimako wani lamari ne da ya dade aka san bangarorin biyu da shi tun da dadewa don haka abune mai kyau a ci gaba da rike lamarin domin ciyar da kasa gaba.

Ya kuma yi godiya ga ministan da bai mance da irin zumuncin da ke tsakaninsu ba duk da ya zama minista amma ya kawo ziyara kamar yadda ya saba a baya.

Sai ya godewa shugaban kasa Muhammadu Buhari kamar yadda ya bayar da sakon gaisuwa a gaya masa.

Daga cikin bakin da suka halarci taron bude bakin sun hada da Fasto Yohanna YD Buru, da yazo da tawagar Fastoci maza da mata inda aka ci aka sha domin karfafa zumunci da zamantakewar da ke tsakanin juna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here