Imrana Abdullahi Daga Kaduna
KWAMANDAN shiyyar a hukuma kulawa da hadurra ta kasa FRSC da ke kula da Jihohin Kano,Kaduna,Jigawa da Katsina Mista Bulus Darwang, ya tabbatar da cewa sun samu nasarar rage yawan hadurran da ake samu a duk fadin shiyyar baki daya.
Bulus Darwang, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar aiki cibiyar yan Jaridu ta kasa reshen Jihar Kaduna domin fadakarwa a kan ayyukan da hukumar FRSC suke aiwatarwa a matakin shiyyar da yake wa shugabanci.
Ya bayar da tabbacin cewa daga cikin kashi 25 daga Dari na alkalumman da ya dace a samu kamar yadda yake kunshe a tsarin hukumar na yawan adadin hadurra sun samu ragowar hadarin da kashi 17 a shiyyar da yake aiki.
Kuma daga cikin kashi 15 na yawan mace mace sakamakon hadari sun samu nasarar kashi 12 na raguwar mace mace sakamakon hadurra.
Ya kuma fadakar da masu ababen hawa da kuma masu sana\’ar saye da sayar da kowace irin Taya da ake amfani da su a ababen hawa da cewa tsawon lokacin yin amfani da su bayan da aka yiyi su tsawon shekaru hudu ne kawai don haka a rika kula a jikin Tayoyin an rubuta a rubuce domin kiyaye hadarin da ka iya faruwa a kowane lokaci ba tare da an gaya ma mai amfani da Taya ba.
\”Muna kara yin gargadi ga daukacin masu abubuwan hawa da su tabbatar suna kulawa da dokokin hanya domin tsira da mutunci da tsare dokar kasa da Lafiya baki daya.