Rabo Haladu Daga Kaduna
\’YAN sanda a jihar Adamawan sun ce an gano wani fitaccen mawakin Hausa da aka sace ranar Juma\’a, jim kadan bayan
ya fitar da wata sabuwar waka da ke Allah- wadai da halayen wasu \’yan siyasa a jihar.
Kakakin \’yan sandan jihar, Uthman Abubakar, ya shaida wa manema labarai cewa an gano Ado Haliru
Daukaka ne a wani kauye mai nisa inda wadanda suka sace shi suka jefar da shi cikin halin galabaita.
A ranar Juma\’ar da ta gabata ne mawakin ya yi batan dabo bayan ya bar gidansa da safe.
Matarsa Malama Hadiza Dauda, ta ce ya fita da zummar zai je shagonsa, amma tun lokacin bai
koma gida ba.
Malama Hadiza ta ce, \’\’Tun daga lokacin muka yi ta kokarin nemansa a waya amma shiru ka
ke ji har inda nan ke motsi.\’\’
Ta ce a iya saninta maigidanta ba shi da abokin gaba, amma ba ta sani ba ko wani ke bin sa da mugun nufi.
Wannan mawaki dai ya dan jima yana haskawa a jihar Adamawa sakamakon wakokin siyasa da yake yawan yi.