Na Hango Fitina A Cikin Bara – Mujahid

0
1590

Imrana Abdullahi Daga Kaduna

AN bayyana irin yadda wasu mutane suka mayar da bara ta zama tamkar wata hanyar rayuwa a matsayin al\’amarin da ke neman ya gagari kundila.

Wani malamin addinin musulunci da ke koyarwa a jami\’ar Ahmadu Bello Zariya Dakta Yahaya Mujahid ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron kungiyar mata musulmi ta FOMWAN karo na 22 da aka yi a dakin taro na gidan tunawa da Sardauna.

Taron da kungiyar ta saba yi a kowace shekara a karshen watan Azumin Ramadana an bayyana shi da alamarin da ya dace.

Dakta Mujahid ya ci gaba da cewa duk da wasu na matukar danganta lamarin Barace barace da cewa harka ce ta addini lallai yana bukatar a dauki matakin gaggawa domin dakile kafin ya zama alakakai baki daya.

\”Saboda kamar yadda kowa ya sani ne idan an bi tsarin musulunci to ba za\’a yi bara ba Sam sam.\”.

Ya kara da cewa sakamakon irin yadda wasu suka dauki al\’amarin Bara har ya zamo ana taba daraja da martabar addinin Islama a tsakanin al\’umma don haka lokacin da za\’a yi sako sako ko duk wani sakaci da lamarin ya wuce.

Ya bayar da misalin irin yadda Imam Buhari ya kasa fitowa cikin jama\’a sakamakon rashin suturar da zai sa domin ya shiga taron mutane domin ya sayar da duk kayan sawarsa ba zai iya fitowa taro ba.

Ya karkare da cewa shi a matsayinsa ya gano fitina a bara don haka ya zama wajibi a tsare al\’umma.

Daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da Mai martaba Sarkin Birnin Gwari Alhaji Zubairu Jibril mai Gwari na II wanda sarkin Kudun Birnin Gwari ya wakilta.

Sai malamai da sauran jama\’a daga ciki da wajen Jihar Kaduna tare da dimbin mata mambobin kungiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here