USMAN NASIDI DAGA Kaduna
A ranar Litinin da ta gabata ce mazauna kauyen Gurguzu da ke kusa da garin Maguzawa a Rigasa cikin karamar Hukumar Igabi a kusa da garin Kaduna suka fada cikin rudani da tashin hankali sakamakon kashe mutanensu hudu da wadansu ’yan bidiga a kan babura suka kai kauyen.
Maharani sun kuma raunata mutum biyu wadanda aka kai su asibiti domin yi musu jinya.
Bayanai daga yankin sun ce lamarin ya auku ne da misalin karfe 6:00 na yamma, kuma babu wanda ya san dalilin kashe wadannan mutane wadannda akasarinsu matasa ne \’yan kasa da shekara 40.
“Lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:50 a lokacin suna cikin gona suna hutawa bayan sun yi Sallar La’asar. Koda maharar suka isa wurin sai suka bude musu wuta haka kawai. Nan take mai gonar da mutum uku suka rasu,” inji wani mazaunin Rigasa da bai so a ambaci sunansa.
Shugaban riko na karamar Hukumar Igabi Malam Jabir Khamis ya ce mutanen unguwar fiye da 500 sun yi hijira daga gidajensu domin tsoro sakamakon karar bindigogin da suka ji.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna, Adamu Ibrahim wanda ya ziyarce sakatariyar ’yan jarida ta jihar ya ce tuni rundunarsa ta aika yankin domin gudanar da binciken ainihin abin da ya faru.