Siffofi 10 Na Matar Da Ba A Mantawa Da Ita Har Abada

    0
    3598

    A yau ranar daya ga watan Shawwal muna dauke da wata makala da ke bayanin irin siffofin mace ta kwarai da za ta yi tasiri a rayuwar mijinta kamar yadda wakilinmu Imrana Abdullahi ya yi hidimar makalar asha karatu lafiya.

    Zaka iya auren mata hudu, amma daya ce zata yi tasiri a rayuwarka — Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

    A cikin nazarin da nake yi yau na ci karo da wata gajeriyar hudubar da Sheikh Aminu Daurawa ya gabatar kan siffofi mata goma da ba a mantawa da su a rayuwa har abada, kuma na ga akwai mahimmanci mu amfana da su a wannan majalisa mai amfani. Babu shakka duk macen da ta samu dacewa da su, za ta cimma babban rabo a duniya da lahira.

    Ina fata ‘yan’uwanmu mata za su karanta, su yi amfani da su. Ya kamata mu sani cewa mace daya ce a duniya take da wuyan samu, amma idan ka samu irinta, kada ka kuskura ka rabu da ita.

    Ya halatta ka auri mace fiye da daya, amma ka sani, mace daya ce kawai, ta ke yin tasiri a rayuwa, wacce ranka kullum zai kasance a kanta. Babbar tambaya a nan ita ce, wacece wannan dayar? Ita ce wadda duk da namiji yake muradin samu a rayuwarsa, ita ce wadda ke koyi da rayuwar shugabar matan duniya kuma diya ga Rasulallahi (SAW), wato Nana Fatima (Allah Ya kara mata yarda). Haka kuma ita ce wadda kowace mace take fata ta zama!

    Ga siffofinta guda goma, kamar haka:

    1.     Matar da ta yarda ita mace ce, don haka ta tanadi duk abin da ake bukata a wajan mace.

    2.    Mace mai hikma da azanci, wacce ta karanci mijinta dakyau, kuma take kaucewa duk abin da zai haddasa matsala a tsakaninsu.

    3.    Mace mai taushin hali da nutsuwa, wacce miji yake jin nutsuwa, idan yana tare da ita.

    4.    Mace da kudi bai dame ta ba, ita mijinta kawai take so, ko da akwai ko babu.

    5.    Mace mai hakuri da juriya, babu gunaguni, babu mita, da kai kara ga iyaye ko kawaye.

    6.    Macen da ta dauki kanta likita, mijinta mara lafiya, domin ya sami kulawa, ta musamman da riritawa.

    7.    Mace mai saurin daukar ishara, tana gane shiru da magana, da motsi da yanayin shigowa da fita, samu da rashi da kuma yanayin da ake ciki a duniya ko a gari.

    8.    Mace mai sakakkiyar zuciya, mara kulli da ramuwa

    9.    Mace mai karawa miji kuzari da karfin hali, a kan kyawawan manufofinsa

    10.  Mace mai rikon amanar aure, da soyayya ga mijinta kawai.

    Da fatan za a yi nazarin wannan huduba da idanun basira, kana a tattauna cikin nizamin hankali da ilmi. Allah yasa mudace

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here