USMAN NASIDI Data Kaduna
Akalla mutum takwas ne suka rasa rayukansu kuma da dama suka ji raunuka sakamakon fada a tsakanin Fulani makiyaya da manoma a garin Koh da ke karamar Hukumar Girie a Jihar Adamawa.
Idan ba a manta ba a makon jiya a garin na Koh ’yan sanda uku sun rasa rayukarsu a lokacin da suka je aikin tsaro don kwantar da ke neman tashi a garin.
Karo na uku ke nan da fada yake barkewa a tsakanin makiyaya da manoma a cikin wata shida da suka gabata.
Fadan farko ya faru ne a watan Janairu na bana, inda mutum 40 suka rasa rayukansu har wani DPO wanda aka kashe lokacin da yake aikin tsaro a garin binikland da ke jihar.
Wadanda lamarin ya auku a kan idonsu sun ce fadan na makon jiya, ya faru ne a lokacin da wadansu makiyaya suka shiga gonar wani manomi dan garin Koh, inda manomin da
ke cikin gonar ya nemi taimako daga mutanen Koh.
Shaidun sun kara da cewa bayan ya nemi taimako sai mutanen garin suka fito suka yi nasarar korar makiyayan, lamarin da ya sa makiyayan suka dawo da tasu tawagar domin yaqi da manoman Koh.
“Wadannan mutum takwas da suka rasu da kuma bakwai da suka ji rauni an kai su asibitin Zinth da ke Yola domin su samu kulawa amma akwai wadansu biyu da nake ganin da qyar su sha,” inji daya daga cikin shaidun.
Wani dan siyasa da ke garin Koh, Mista P.P. Elisha ya tabbatar da faruwar fadan, kuma ya ce ya rasa
’yan uwansa biyu a fadan wanda a cikinsu akwai dan sanda daya.
Kakakin ’Yan sandan Jihar Adamwa, DSP Abubakar Othman ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce mutum daya ne kawai ya rasu a fadan na makiyaya da manoman.
Othman ya ce qura ta lafa domin an aike da ’yan sanda da dama garin Koh saboda tabbatar da zaman lafiya.